Hukumar Raya Neja Delta (NDDC) ta gargadi ‘Yan Najeriya game da ayyukan ‘yan damfara, a suna ba da tallafin karatu na gaba da Sakadare ga wadanda ba su ji ba gani ba.
Darakta mai kula da harkokin kamfanoni na NDDC, Misis Seledi Thompson-Wakama, wacce ta yi wannan gargadin a cikin wata sanarwa, ta bayyana cewa, ‘Yan damfara sun rika neman kudi daga jama’a bisa hujjar samun gurbin tallafin karatu.
“An jawo hankalin NDDC ga sakon imel na yaudara da kuma sakonnin da aka aiko zuwa ga masu neman takardar da tallafin karatu na kasashen waje na hukumar,” in ji ta.
Thompson-Wakama ya bayyana cewa, sakon na bogi ne, da ake zargin an aiko su ne, daga nddcregistry@gmail.com kuma suna ikirarin cewa, sun fito ne daga ‘Board Registry na NDDC, suna gayyatar wadanda aka karbi don tantance su.
A cewarta, atisayen da ake zargin zai a gudanar daga ranar 19 ga watan Mayu zuwa 21 ga watan Mayu, a titin Bishop Oluwole, Victoria Island, Legas.
“An shawarci jama’a da cewa, NDDC ba ta da alaka da wannan tsarin zaben na yaudara ne,” in ji ta.
Ta kara da cewa “An shawarci masu neman aiki da karfi da su yi watsi da duk wani sakon da ba a nema ba, da ke neman kudi, gayyata, bayanai masu mahimmanci, ko bayar da wuraren da tallafin karatu a wajen tsarin NDDC na hukuma,” in ji ta.
Thompson-Wakama ya bukaci duk wanda ya samu irin wadannan sakwannin na bogi da ya gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro da suka dace domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin gaggawa.
Ta karfafa ‘yan Najeriya masu sha’awar shirye-shiryen NDDC da su yi amfani da tashoshin sadarwa na NDDC kawai.
Ta kara da cewa “An shawarci masu neman aiki da su yi watsi da duk wani sakon da ba a nema ba, da ke neman kudi da gayyata da bayanai masu mahimmanci, ko bayar da wuraren tallafin karatu a wajen tsarin NDDC na hukuma,” in ji ta.
Thompson-Wakama ya bukaci duk wanda ya samu irin wadannan sakwannin na bogi da ya gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro da suka dace domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin gaggawa.
Ta karfafa ‘Yan Najeriya masu sha’awar shirye-shiryen NDDC su yi amfani da tashoshin sadarwa na NDDC kawai.
“Har ila yau, muna ba da shawara ga tsoffin wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen hukumar da masu neman izini da su tabbatar da bayanan ta hanyar yanar gizon NDDC: www.nddc.gov.ng.” Daraktan NDDC ta kammala
NAN/Aisha.Yahaya, Lagos